TSAKANIN KWAKWALWA DA ZUCIYA 4
ASALIN TUNANI - TSAKANIN KWAKWALWA DA ZUCIYA. WA KE SAMAR DA TUNANI? PART FOUR
Yadda Tunani ke Samuwa Daga Kwakwalwar Dan Adam
A yau muna dauke ne da bayanai kan binciken malaman kimiyyar zamani, da sakamakon da suka samu da a cewarsu lallai tunani na samuwa ne daga kwakwalwar dan adam. Wannan shi ne ra'ayin malaman kimiyyar zamani. Shi ya sa ma daya daga cikinsu mai suna Albert Einstein yake cewa: "Wannan duniyar da muke zama a cikinta mun kera ta ne ta hanyar tunaninmu; don haka babu yadda za a yi ta sake canzawa sai mun canza tunaninmu." Wannan kalma ta tunani da ya ambata yana ishara ne ga tunanin da ke darsuwa ko samuwa daga kwakwalwa, kamar yadda sakamakon bincikensu ya nuna musu.
Sai dai kuma, duk da wannan sakamako da suka fitar, har yanzu suna ganin cewa babu bangaren jiki mai wuyar sha'ani wajen fahimta irin kwakwalwar dan adam. Domin duk tsawon zamani da duniya ta dauka ana gudanar da bincike kan yadda tsari da kintsin kwakwalwa yake, har yanzu abin da aka gano a ilimance dangane da kwakwalwa da irin yadda take gudanar da aikinta, bai wuce kashi 5 ba cikin 100. Daga cikin bangarorin da fahimtar tsarinsu da yadda suke samuwa yafi komai wahala, akwai tsarin tunani, da kuma yadda "hankali" ke samuwa a tare da mutum. Shin, daga kwakwalwa yake ko daga ina? Shi kanshi wannan wani bincike ne mai zaman kansa. Domin idan ka bude kwakwalwar dan adam, kamar yadda bayani ya gabata a kasida ta biyu, ba abin da za ka gani sai tarin jijiya da yadi, da hanyoyin jini, da kuma romon kwakwalwa, watau Brain Protein. Amma kuma, a cewarsu, wadannan bangarori ne ke samar da ji, da gani, da dandano, da tabawa, da fahimta, da hardace abubuwa, da yanke hukunci kan wasu ra'ayoyi biyu, da dai sauransu. Babu wanda ya fito fili ya bayyana irin sarkakiyar da ke dauke cikin kwakwalwa irin wani masanin kimiyya mai suna Gottfried Leibniz. Ya nuna cewa babu abu mafi wahalar fahimta irin yadda tunani da fahimta ke samuwa daga kwakwalwar dan adam, musamman ganin cewa ba wani girma bane da ita, sannan idan ka bude ciki in ban da yadi da jijiyoyi da romon kwakwalwa babu abin da za ka gani. Har ya ba da misali da babban injin da ke sarrafa na'urar makamashin iska, watau Windmill. Yace idan ka bude ciki babu abin da za ka gani sai karafa; wani akan wani, ko wani na juya wani. Wannan zance nashi ya shahara a tsakanin masana, har a karshe ake masa lakabi da: Leibniz Mill.
Bangarori Masu Alaka da Tunani
Kafin mu yi nisa, kwakwalwa na da bangarori daban-daban. Amma a jimlace malaman kimiyya kan kasa kwakwalwa ne zuwa gida biyu. Da bangaren dama wanda suke kira Right Hemisphere. Sai bangaren hagu da suke kira Left Hemisphere. Bincike ya tabbatar da cewa jijiyoyin da suka taso daga kwayoyin idanun dan adam suna like ne a kwakwalwa. Jijiyoyin idon bangaren hagu na like ne da bangaren kwakwalwa na dama. Su kuma jijiyoyin idanu na dama suna like ne da bangaren kwakwalwa na hagu. Bayan haka, bincike ya nuna cewa bangaren kwakwalwar dan adam ta dama, ita ce ke sarrafa bangaren jikinsa na hagu. Bangaren kwakwalwarsa ta hagu kuma ke sarrafa bangaren jikinsa na dama.
Bangaren kwakwalwa mai lura da tsarin tunani da fahimtar yanayi da yanke hukunci, shi ne bangaren da ke gab da goshi, wanda malaman kimiyya ke kira Cerebral Cortex. Daga cikin wannan bangare akwai tsagin da ake kira Frontal Cortex, wanda ke da alaka da wani gungun tsarin da ke lura da sha'awa, da sinsino, da fahimta, da tunani, da barci, da jin zafi, da jin dadi, da gamsuwa, da jima'i, da sauran al'amuran da suke da alaka da dabi'ar jiki. Wannan gungu na tsarin kwakwalwa shi ake kira da suna The Limbic System, kuma yana shimfide ne a kasa daga ciki, ya kuma bazu zuwa bangaren kwakwalwa na hagu da dama, da bangaren goshin dan adam. Daga cikin bangarorin wannan gungu na Limbic da ke lura da dabi'a, bangaren Frontal Cortex ne ke lura da tsarin tunani sakakke, watau Abstract Thoughts. Shi ne ke lura da karfin tunani kuma mai sa a iya yanke hukunci, ko daukan zabi a tsakanin nau'uka ko jinsin abubuwa guda biyu.
Amma kafin haka ya samu a wannan bangare na Frontal Cortex, sai ya samu bayanai kan abin da ya danganci nau'in tunanin da zai yi. Wadannan bayanai kuwa suna samuwa ne ta hanyar kwayoyin halittar kwakwalwa, watau Brain Cells, masu dauke da sakonnin sadarwa ta hanyar maganadisun lantarki da ke samuwa a jijiyoyinsu da ake kira Glia a kimiyyance. Wannan jijiya ta Glia ce ke dauko bayanai daga jijiyoyin da suka fito daga idanu (wajen gani), da wadanda suka fito daga kunnuwa (wajen ji), da wadanda suka fito daga harshe (wajen dandano), da wadanda suka fito daga hanci (wajen shaka), sai wadanda suka fito daga fatar jiki (wajen fahimtar suka, ko yanka, ko duka, ko duk wani abin da ya taba jikin da adam). Wadannan su ne kafofin samar da bayanai guda biyar da ke jikin dan adam.
Da zarar bangaren Glia ta tattaro wadannan bayanai, sai ta hada kai da jijiyoyin sadarwar kwakwalwa, watau Neurons, da kuma sinadaran Hormones. Nan take sai su sana'anta wadannan bayanai da suka taro don samar da tunani da ji irin na zuci (watau Emotions), kamar yadda Mark Treadwell, wani masanin kimiyya dan kasar New Zealand ya tabbatar. Idan bayanan masu alaka da zartar da hukuncin wani aiki ne na gabar jiki a aikace, nan tace sai jijiyoyin bangaren sadarwar jiki (watau Motor Neurons) su zaburar da su wajen aikatawa. In kuka ne, nan take sai dan adam ya kece da kuka. In dariya ne, ko bakin ciki ko annashuwa, duk nan take suke samuwa. Wannan nau'in tunani wanda ke samuwa ba tare da son dan adam ko yardarsa ba, shi yafi yawa daga cikin nau'ukan tunani da adam ke yinsu a kullum.
Malaman kimiyya sun kiyasta cewa a cikin duk dakika guda, kwakwalwar dan adam kan taro bayanai sama da miliyan biyu ta wadannan hanyoyin samar da bayanai biyar. Daga cikin miliyan biyu din nan, kashi biyar cikin dari ne kadai dan adam ke iya sarrafa su don yin tunani da nufinsa. Amma duk sauran na tafiya ne wajen tunani irin na dabi'a, wadanda Allah ya tsara halittarsa a kansu. Ire-iren wadannan tunani ma dan adam ba ya sanin ya yi su. Saboda tsarin da suke gudana, da saurin gudanuwarsu. Misali, irin waige, da motsa yatsun hannu, da bita idanu, da hadiye yawu, da neman abinci idan yunwa ta karato, ko neman ruwan sha idan kishirya ta koro shi. Dukkan wadannan abubuwa suna bukatar tunani kafin yinsu. Amma da yawan lokuta dan adam ba ya taba tuna cewa ga lokacin da ya yanke shawarar aikata su kafin suka faru. Sai dai yace kawai yayi su lokaci kaza. Wasu ma ba ya iya tuna ya gudanar da su. To amma, ta yaya malaman kimiyya suka gano wadannan al'amura?
Tsarin Bincike Don Tabbatar da Tunani
Akwai hanyoyi uku da malaman kimiyya suka bi ko suke bi a halin yanzu wajen fahimtar tsarin tunani da duk wani abin da ya shafi gudanuwar kwakwalwar dan adam. Hanya ta farko ita ce ta hanyar amfani da kwakwalwar wasu halittu masu kama da na dan adam, irinsu Birai, da Gwaggon biri da sauransu. Suna yin haka ne saboda akwai kamaiceceniya tsakaninsu, duk da cewa kwakwalwar dan adam ta bambanta nesa ba kusa ba da na wadannan halittu. Sukan fahimci wasu abubuwa ta hanyar wannan kamaiceceniya dake tsakaninsu.
Hanya ta biyu ita ce idan hadari ya faru wanda ya shafi kwakwalwar dan adam. Misali idan ya samu buguwa a wani bangare na kansa har abin ya kai ga kwakwalwa. Da zarar ya warke sai su rika lura da shi, idan aka ga ya kasa magana, ko ya kasa hankaltar yanayin da yake ciki – ya zama wani sususu misali – ko ya kasa ji, ko ya kasa tuno wasu abubuwa da ya sani a baya, sai su fahimci cewa lallai wannan bangaren da ya samu buguwa ne ke da alhakin sarrafa abin da ya rasa na kudura a matsayinsa na cikakken dan adam. Sukan nuna wannan hatta a fina-finansu. Misali, akwai wani fim mai suna The Bourne Identity, a cike yake da irin wannan yanayi na bincike.
Sai hanya ta uku, watau hanyar binciken zamani kenan, wanda ya kunshi amfani da na'urorin sadarwa masu sinsino ko gano ko dauko hoton yanayin da kwakwalwa ke gudanuwa a wani lokaci na musamman. Daga cikin irin wadannan na'urori akwai na'urar Electroencophalography (EEG), wacce ake amfani da ita wajen gano yanayin harbawan sinadaran lantarki (Electrical Impulses) da shawaginsu a kwakwalwar dan adam. Sai na'ura ta biyu mai suna Magnetoencephalography (MEG), wacce ke darsano sinadaran maganadisun kwakwalwa, watau karfinsa wajen jawo ko sinsino yanayin da yake ciki. Wadannan sinadaran maganadisu su ake kira Brain Magnetic Field.
Wadannan, a takaice, su ne hanyoyin da masana ke bi wajen gudanar da bincike kan abin da ya shafi kwakwalwar dan adam. Da wannan, kamar yadda bayani ya gabata a baya, suke tabbatar da cewa lallai tunani na samuwa ne daga kwakwalwar dan adam. A mako mai zuwa za mu tattauna kan nassoshin Kur'ani da abin da suke tabbatarwa wajen samuwar tunani ga dan adam. A ci gaba da kasancewa tare da mu.
Mahangar Musulunci Kan Asalin Tunani
A makon jiya mai karatu ya ji ra'ayi da binciken Malaman kimiyyar zamani kan abin da ya shafi asali ko samuwar tunani tsakanin kwakwalwa da zuciyar dan adam. A nasu bangaren, basu yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa tunani na samuwa ne daga kwakwalwa. Sun tabbatar da hakan ne dangane da bayanai da sakamakon binciken da suka samu tsawon zamani, duk da cewa har yanzu abin da suka sani na ilmi kan aikin kwakwalwa da matsayinsa wajen hankaltar abubuwa, da tunani, da fahimta, duk bai wuce kashi biyar ba cikin dari. To amma, kasancewar al'adarsu ce su tabbatar da abu bayan sun samu tabbaci daga sakamakon bincikensu, shi yasa suka yi haka. A gaba za mu kara kutsawa dakin bincike don fahimtar ko akwai wani sabanin ra'ayi ko burbushinsa, da ke nuna akasin sakamakon wannan bincike da suke dogaro a kai a yau.
A yau cikin yardar Allah ga mu dauke da bayani kan mahangar Musulunci dangane da abin da ya shafi tunani; shin, daga zuci yake samuwa ko daga kwakwalwa? A mukaddimar da muka gabatar kan nau'ukan ra'ayoyi dangane da haka, mun fahimci cewa, ta la'akari da ayoyin Kur'ani da wasu hadisai na Manzon Allah (tsira da aimincin Allah su kara tabbata a gare shi), tunani na samuwa ne daga zuci, sabanin abin da malaman kimiyya suke tabbatarwa a yanzu. Amfanin wannan kasida ta yau shi ne tabbatar da hakan ta hanyar kawo nassoshin Kur'ani masu Magana kan hakan, da na hadisai. Domin su ne bayanan da shakku ko kokwanto ba ya shiga cikinsu, saboda tabbacin da ke tattare da asalinsu. Kuma tunda mai zancen shi ne ya halicci dan adam wanda muke Magana kan tsarin halittarsa, ashe kuwa babu wanda zai fahimtar damu gaskiyar abin da ya dangance shi sai Mahaliccinsa. Bayan haka, za mu ji mahangar Malaman musulunci kan ma'anonin da suke baiwa wadannan ayoyi ko hadisai dangane da abin da muke nema na ma'ana a tare dasu.
Kalmar "Zuciya" a Nassin Kur'ani
Daga cikin gabobi ko sassan jikin dan adam, babu bangaren da Allah ya ambace shi karara, da sunaye daban-daban irin zuciyar dan adam. Wannan a fili yake ga duk makarancin Kur'ani, masani. Shahararriyar kalma ita ce wacce a asali take nufin Kalmar zuciya karara, a harshen Larabci. Wannan kalma ita ce: Al-Qalbu. Allah ya kawo ta a sigar tilo, watau Al-Qalbu, ya kuma kawo ta a sigar jam'i, watau Al-Quloob. Wannan ita ce Kalmar da tafi shahara cikin kalmomin da aka yi amfani da su wajen ambaton zuciyar dan adam; musulmi ne ko kafiri, Annabi ne ko wani gama-garin mutum.
Kalma ta biyu da Allah yayi amfani da ita don nufin zuciya ita ce kalmar: Al-Fu'aad. Ita ma ta zo a sigar tilo, watau Al-Fu'aad, sannan ta zo a sigar jam'i, watau Al-Af'idah. Wannan kalma ita ma ta dan shahara a cikin Kur'ani. Sai kalma ta uku, watau kalmar As-Sadr. Kamar sauran kalmomin da suka gabace ta, ta zo a sigar tilo da jam'i ita ma. Watau ko dai ta zo a As-Sadr, ko kuma ka ga tazo da suna As-Sudoor, watau jam'in Sadr kenan. Asalin ma'anar Sadr na nufin "kirji" ne a harshen Larabci. Amma saboda alakar da ke tsakanin kirji da zuciya, dangane da abin da Allah ke son tabbatar mana don mu fahimta a aya, shi yasa duk masu tafsiri ke hada alaka tsakaninsa da zuciya, amma sukan fassara kalmar ne da ma'anarta na asali (watau kirji). Domin kirji ne farfajiyar zuciya, kuma ganin cewa duk abin da ke cikin farfajiyar nan yana tasirantuwa da abin da ke ciki, kuma zuciya ce gabar da tafi tasiri cikin gabobin da ke cikin kirji (tun da a wasu ayoyin an ambace ta karara), sai malamai su dauka kai tsaye zuciya ake nufi. Allah shi ne mafi sanin sirrin da ke cikin ma'anonin kalmominsa.
Wadannan kalmomi, a takaice, su ne ke ishara ga zuciya a cikin Kur'ani. Sannan sun maimaitu a wurare da dama, wanda hakan ke nuna matukar muhimmancin zuciya ga dan adam wajen fahimta ko rashin fahimtar sakon shiriya da Allah ya aiko Manzonsa da shi. Kafin mu yi nisa, mu fahimci cewa yawan ambaton abu, a tsarin zance, na nuna lallai akwai wani muhimmanci – na bayyane ko na boye – da wannan abin ya mallaka ko yake yi.
Nau'ukan Zukata da Dabi'unsu
Kafin mu yi bayani kan na'ukan zuciya, yana da kyau mu yi bayani kan dabi'un zuciya. Da farko dai, zuciya abu ne guda daya, watau dunkulen nama da ke bangaren kirjin dan adam na hagu, wacce ke aikin famfon jini, kamar yadda bayanai suka gabata. Kuma, kamar yadda Allah ya fada cikin Kur'ani, bai taba halittar wani dan adam da zuciya guda biyu a kijinsa ba. Wannan sunna ce wacce ya tsara wa kansa, cewa kowane dan adam zuciya daya ake halittarsa da ita. Daga cikin dabi'un zuci da muka sani a al'adance, akwai ji irin na tausayi, da so, da kauna. Wadannan su ne manyan dabi'un da a al'adance muke danganta su ga zuciya. Hatta masana fannin kimiyya da wannan suka san zuciya, duk da cewa ko a kimiyyance ba za su iya nuna alamar da ke nuna samuwar soyayya da kauna da suke danganta su gare ta ba (tunda ba abubuwa bane da ake iya ganinsu); sabanin hujjar da suke da ita kan kwakwalwa.
A daya bangagren kuma, Musulunci ya sanar da mu kari a kan wasu halayyar da muka sani dangane da zuciya. Wadannan sun hada da: imani, da kafirci, da munafunci, da tunani, da fahimta, da rashin fahimta, da karbar gaskiya, da kin gaskiya, da shiriya, da karkata, da sabo, da niyya, da tsarkakuwa, da baci ko dauda, da karamci, da fushi, da rashin damuwa, da tsoro, da damuwa, da bakin ciki, da shakka, da kokwanta, da keta, da tawaye, da nadama, da tabbaci, da rashin tabbaci, da jiji-da-kai, da kishi, da kuma girman kai. Wadannan su ne yanayi da dabi'un zuciya, kamar yadda nassoshin Kur'ani da hadisai ke nunawa. Shi yasa suka kasa nau'ukan zukata zuwa kashi biyu; da zuciya lafiyayya ko kubutacciya daga kowane irin cuta, wacce ke dauke da farin ciki, da kwanciyar hankali, da imani, da gaskiya, da mika lamura zuwa ga Allah, da kuma zuciya mara lafiya, wacce ke dauke da cututtuka irinsu kafirci, da bidi'a, da shakka kan sakon Allah, da kokwanto, da girman kai, da zalunci, da yawan sabo, da sauran matsaloli makamantansu. Wannan rabe-rabe ne da malaman Musulunci suka yi, dangane da bayanan da suka zo cikin ayoyin Kur'ani da hadisan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ingantattu.
Dangane da bayanan da suka gabata, idan muka yi dubi sai mu ga cewa a zahirin lafazi da yanayi, wannan zuciyar da muke dauke da ita a kirjinmu na bukatar karin bayani kan ayyukan da take yi. Domin abin da muka sani kawai shi ne, tana aikin rarraba jini ne a jikin dan adam, wanda hakan ke taimakawa wajen tabbatar da rayuwarsa. Wannan ta sa ra'ayoyin malaman musulunci suka sha bamban wajen ma'anar kalmar "Al-Qalbu" ko "Al-Fu'aad" a cikin Kur'ani mai girma. Shin, akwai wata zuciya ce tattare da asalin zuciyarmu wacce ke gudanar da wadannan ayyuka amma ba a ganinta, ko kuma ita din ce ke dukkan ayyukan, a bisa kudura da ganin damar Ubangiji? Ko kuma dai kawai anyi amfani da kalmar ne don nufin wani abu daban, watau Majaaz kenan?
Vulnerability is the essence of romance. It’s the art of being uncalculated, the willingness to look foolish, the courage to say, ‘This is me, and I’m interested in you enough to show you my flaws with the hope that you may embrace me for all that I am but, more important, all that I am not.’
---Ashton Kutcher