TSAKANIN KWAKWALWA DA ZUCIYA 5
ASALIN TUNANI - TSAKANIN KWAKWALWA DA ZUCIYA. WA KE SAMAR DA TUNANI? PART FIVE
Sabanin Ra'ayi kan Ma'anar Zuciya a Larabci
Kamar sauran ayoyin da suka zo kan wasu mas'alolin shari'a, Malaman tafsiri sun sha bamban wajen fahimtar ma'anar kalmomin da ke nuni zuwa ga zuciya a Kur'ani da Hadisai ingantattu. Wasu sun dauki kalmar a zahirin ma'anarta kamar yadda Allah ya kawo ta, basu mata tawili ba. Ma'ana, basu karkatar da ma'anarta zuwa ga wani abu daban ba. Wasu kuma sun dauki kalmar zuciya ("Al-Qalbu", ko "Al-Fu'aad", ko kuma "As-Sadr") a matsayin Majaaz ne. Watau kalmar da ke wakiltar wani abu daban, amma ba ita ake nufi ba. Suka ce abin da ake nufi shi ne "Hankali" ko kuma "Basira."
Bayan haka, wadanda basu yi wa wadannan ayoyi ko kalmomi tawili ba wajen tafsiri, suna dogaro ne da cewa, daga cikin ayoyin da Allah ya ambaci zuciya, akwai inda ya ambace ta yana mai danganta ta ga tunani ko hankaltar abubuwa. Har wa yau, akwai kuma ayoyin da Allah ya ambaci kalmar zuciya tare da mahallin da take, watau kirji kenan. In kuwa haka ne, a cewar masu wannan ra'ayi, lallai akwai alakar da ke nuna dangantaka a tsakaninsu, dangantaka mai karfi kuwa. Domin Allah ba zai ayyana abu, tare da muhallinsa, ya kuma danganta masa wani aiki na musamman ba, face akwai hakan tare da abin da Allah ya ambata. Domin daga cikin sifofin Allah madaukakin sarki shi ne, Mai hikima ne shi, yana dora kowane abu ne a mahallinsa; ba ya yin wani zance wacce ba ta bayar da fa'ida.
Suka ce wuri na farko da Allah ya ambaci zuciya yana alakanta ta da tunina shi ne cikin Suratul A'araaf, aya ta 179, inda yake cewa: "Kuma lalle ne hakika, mun halitta, saboda Jahannama, masu yawa daga cikin aljannu da mutane; suna da zukata, ba su fahimta da su…." Suka ce Allah ya ambaci zukata (na mutane da aljannu), sannan yace ba su fahimta da su. Fahimta kuwa, a cewarsu, ba ta samuwa sai ta hanyar tunani. Wuri na biyu na cikin Suratul Taubah aya ta 87, inda Allah ke cewa: "…Sun yarda da su kasance tare da mata masu zama (a cikin gidaje). Kuma aka rufe a kan zukatansu, saboda haka, su, ba su fahimta." A nan Allah na ishara ne ga munafukan madina da suke kin zuwa yaki, da sakamakon da ya biyo bayan wannan mummunar akida tasu, ga zuciyarsu. Ma'anar da wannan aya ke bayarwa iri daya ne da wanda ta gabace ta. Sai wuri na uku cikin Suratun Nahali aya ta 108, inda Allah ke cewa: "…wadancan ne wadanda Allah ya bice hasken zukatansu da jinsu da gannansu. Kuma wadancan su ne gafalallu." Suka ce wannan aya ma tana nuna cewa lallai zukata na yin tunani. Domin idan babu tunani, babu yadda za a yi gafala, ko shagala da wani abu mai muhimmanci, ya samu. Sai wuri na hudu cikin Suratul Israa'i aya ta 36, inda Allah ke cewa: "Kuma kada ka bi abin da ba ka da ilimi game da shi. Lalle ne ji da gani da zuciya, dukkan wadancan, (mutum) ya kasance daga gare shi wanda ake tambaya." Suka ce wannan ke nuna cewa lallai zuciya na tunani. Domin an hana mutum yanke hukunci ne da jahilci. Idan kuwa zuciya ta zama babu ilimi a cikinta, to, za a rasa yakini (watau karfin tabbaci da irada) a tare da ita. Idan aka rasa yakini a cikinta, to babu abin da zai maye gurbin ilimi sai jahilci. Shi kuma jahilci alamunsa su ne shakku da rashin tabbas, da dimuwa. Su kuma wadannan dabi'u ko yanayin zuci suna samuwa ne ta hanyar tunani. Idan babu tunani, babu yadda za a yi a samu shakka ko dimuwa irin ta zuci.
Sai wuri na biyar, cikin Suratul Kahfi aya ta 28, inda Allah ke cewa: "…kuma kada ka bi wanda muka shagaltar da zuciyarsa daga hukuncinmu, kuma ya bi son zuciyarsa…" Mun yi bayani a baya cewa babu yadda za a yi a samu shagala ba tare da tunani ba. Sai wuri na shida cikin Suratul Hajji aya ta 46, inda Allah ke cewa: "Shin, to, basu yi tafiya ba a cikin kasa, domin ya zama suna da zukata wadanda za su yi hankali da su, da kunnuwa da za su saurare da su a tare da su? Domin lalle ne idanun ba su makanta, amma zukata wadanda ke a cikin kiraza su ke makanta." Suka ce wannan aya na nuna abu biyu. Na farko Allah ya kalubalanci kafirai da suyi tafiya a cikin kasa su ga yadda ya hallakar da wasu al'ummomin da suka gabace su, wannan zai sa su hankalta da zukatansu. Hankalta da abu kuma, kamar yadda muka sani, ba zai yiwu ba sai ta hanyar tunani. Ba wai su kalli abin su san yana nan ake nufi ba, ba irin wannan hankaltar ake nufi ba. Ana nufin su dauki darasi, su kokkoma da zukatansu kan abin da suka gani. Wannan kuwa shi ake kira tunani. Abu na biyu shi ne makantar zuci, wadda ke cikin kiraza. Ma'ana zuciyar da muka sani din nan dai, ita Allah ke nufi, a cewarsu. Sai wuri na bakwai da ke cikin Suratu Muhammad, aya ta 24, inda Allah ke cewa: "Shin to, ba za su yi tunani bane kan Kur'ani, ko kuwa a kan zukatansu akwai makullansu ne?" Wannan aya tana magana ne kan tunani dangane da ayoyin Kur'ani, da gaskiyar zantukan da ke cikinsa. Allah ya ce ko akwai makullai ne da suka kulle zukatan kafirai, da har suka kasa yin tunani kan Kur'ani? A nan Allah ya ambaci rashin tunani, ya alakanta shi da kullewar zuciya. Wannan ke nuna da zuciyar a bude take, da tunani ya samu.
Sai wuri na karshe cikin Suratun Naas aya ta 5, inda Allah ke cewa: "…wanda ke sanya wasuwasi a cikin kirazan mutane." Wannan aya tana magana ne kan tasiri da gamewar wasuwasin shedan ga zuciyar dan adam. Sai aka ambaci mahallin da zuciyar take, watau kirji kenan, don nuna cewa lallai wasuwasin shedan na da gamewa da kuma tasiri mai karfi wajen sabo. Shi wasuwasi wani irin zancen zuci ne mai dauke da umarnin aikata sabo, wanda bawa ke ji a tare da shi. Duk sadda ka ji kana son ka aikata wani aikin sabo, to ka san cewa lallai wannan jin da kake ji a zuciyarka, wasuwasi ne na shedan. Wannan, a cewarsu, alama ce da ke nunawa a fili karara, lallai zuciya na tunani. Domin da ba ta tunani babu yadda za a yi dan adam ya bijire wa dukkan wasuwasin shedan, wanda kuma a halin yanzu ba haka lamarin yake ba. Ma'ana ba dukkan wasuwasin shedan bane yake tasiri wajen sa dan adam ya aikata sabo, in kuwa haka ne, kenan ashe zuciyar dan adam na tunani, wajen tantance irin umarnin da take samu a cikinta, kafin ta baiwa gabobin jiki umarnin aikatawa. Bayan haka, akwai hadisin Nu'umanu dan Bashir wanda a karshensa Manzon Allah ke cewa: "…kuma lallai a cikin jiki akwai wani gudan tsoka; idan ya gyaru, jiki gaba dayansa ya gyaru. Kuma idan ya baci, to, jiki gaba dayansa ya baci. Ku saurara, ita ce zuciya." Dukkan wadannan nassoshi na ishara ne zuwa ga wannan zuciyar da ke cikin kirjinmu, kamar yadda yazo karara a cikin wannan hadisi.
Tantance Hakikanin Lamarin
Daga bayanan da suka gabata, za mu fahimci cewa lallai akwai wani lamari tattare da wannan bangaren jiki da ake kira zuciya; shin, da ra'ayin masu cewa "hankali" ake nufi da kalmar "Al-Qalbu", ko na masu cewa hakikanin "Zuciyar" ake nufi. Domin a cikin Kur'ani an danganta "hankali" ga zuciya. An danganta "tunani" ga zuciya. An danganta "rai" ko "ruhi" ga zuciya. An danganta "An-Nafs" (watau "zati" ko "hakikanin mutum") ga zuciya. An kuma danganta "fahimta" ga zuciya. Dukkan wadannan kalmomi an kawo su a wurare daban-daban, a sigogi daban-daban, inda kalmar "Al-Qalbu" ke wakiltarsu, kamar yadda wasu malamai suka fassara. Amma abin da aka fi danganta shi ga zuciya shi ne "hankali". To, ko ma dai mene ne, akwai wani sha'ani da ke tare da wannan zuciya da Allah ya halitta mana. Domin yawan Ambato – a Kur'ani, da Hadisi, da zantukan Malamai, da littattafansu, da kasidunsu – duk yana tabbatar da haka.
Wannan ishara da nassoshin shari'a suka yi ga zuciya ya sa manyan Malaman musulunci gaba daya sun mayar da hankulansu zuwa ga wannan bangare na jiki. Suna masu danganta ayyuka daban-daban gare ta, wadanda suka shafi halayya da dabi'unta – irinsu imani, da taqawa, da yarda, da kunya, da kara, da tawakkali, da sauransu. Kari a kan haka, sukan hada da "tunani", daga cikin ayyukan da suka shafi zuciya. Wannan a fili yake cikin rubuce-rubucensu. Abdullahi bn Mubaarak, daya daga cikin manyan magabata ya rubuta littafi mai suna: "Az-Zuhd", mai dauke da bayanai kan dabi'un zuci da za su taimaka wa musulumi rage burinsa a rayuwa, don fusktanr lahira. Imamul Ghazaali, Abu Haamid, shi ma ya yi bayani mai tsawo a shahararren littafinsa mai suna: "Ihyaa'u Uloomad Deen", da wani littafi dan karami mai suna: "Mukaashafatul Quloob" inda a ciki ya ware babi na musamman kan tunani, wanda hakan ke nuna cewa lallai tunani na daya daga cikin ayyukan zuciya. Bayan Ghazaali sai Abul Qaasim Al-Qushairee, a cikin shahararren littafinsa mai suna: "Ar-Risaalatul Qushairiyyah." Wanann littafi na dauke ne da bayanai kan ayyukan zuciya, wadanda mutum zai lazimce su don gina kyakkyawar alaka tsakaninsa da Allah. Bayan shi sai Al-Imam Ibn Al-Qayyim, daya daga cikin manyan malaman kasar Sham a karni na 7. Ya yi bayani mai tsawo a cikin littafinsa mai suna: "Madaarijus Saalikeen, Baina Manaazili Iyyaaka Na'abudu wa Iyyaaka Nasta'een," wanda sharhi ne na littafin Imamul Harwee kan dabi'un zuci, masu karfafa imani da alaka tsakanin bawa da Ubangijinsa. A cikin littafin ya ware babi na musamman kan tunani, ya kuma alakanta hakan ga zuciyar bawa, don samun kyakkyawar saitin imani.
Daga cikin malaman wannan zamani akwai Sheikh Muhammad bn Saalih Al-Munajjid, ya rubuta littafi mai suna: "A'amaalul Quloob," watau "Ayyukan Zukata." A ciki ya ware babi musamman kan tunani, ya kuma kawo wasu daga cikin ayoyin da muka yi bayani kansu a baya. Daga shi sai Dakta Khaalid bn Abdulkareem Al-Laahim, farfesa mai karantar da fannin karatun Kur'ani a Jami'ar Muhammad bn Sa'ood na kasar Saudiyyah. Ya rubuta littafi mai suna: "Qiraa'atun Bi Qalbin," ma'ana: "Tsarin Karatu da Zuciya." A shafi na 5, ya kasa nau'ukan karatu, ta la'akari da wajen yinsu, zuwa kashi uku. Kashin farko shi ne yin karatu a bayyane, wanda ya kunshi motsa labba da harshe, da fitar da sautin da ake ji. Sai kashi na biyu da ya kunshi yin karatu a asirce, ta hanyar motsa labba da harshe, amma mai karatu kadai ke jiyar da kansa. Sai kashi na uku wanda ya shafi yin karatu cikin sirri ba tare da motsa labba da harshe ba, sai dai zuciya kadai. Ya kuma kasa nau'in karatu da zuci zuwa kashi uku; na farko yin karatu a asirce ta hanyar amfani da idanu da kuma zuciya. Na biyu ta hanyar amfani da zuciya da tsantsar hadda da aka yi a baya. Na uku kuma yin amfani da zuci kadai. Wannan, a cewarsa, tsantsar tunani ne. A shafi na 6, ya kasa nau'ukan zancen zuci zuwa kashi uku. Na farko shi ne yin magana da zuci kadai, wannan tunani kenan. Na biyu shi ne yin zance da zuci da kuma harshe; ya zama zancen zuci ne harshe ke furutawa. Sai na uku, watau yin zancen zuci da harshe, amma ya zama zancen harshe ya saba wa abin da zuciya ke furutawa (ko tunani ko tattaunawa a kai) – wannan, a cewarsa, shi ne munafunci, wanda da shi ne Allah ya sifata munafukai kan abin da ya shafi imani.
Abubuwan Da Ke Dabaibaye da Zuciya
Daga bayanan da suka gabata za mu fahimci lallai zuciya, wato wannan gudan tsoka da ke kirjinmu, tana da abubuwa da yawa da suka dabaibayeta, masu sa a ambace ta maimakon a ambace su. Wannan ba ya nuna cewa ita kanta ba ta da wani tasiri, a a, akwai alamun ita ma tana da nata tasirin. Ababen da suka dabaibaye zuciya su ne: "Hankali" (Mind/Sense of reasoning), da "Ruhi" ko "Rai" (Soul), da "An-Nafsu," watau "zati" ko "hakikanin dan adam" (Self), da "Fahimta" (Understanding/Comprehension), da kuma "Al-Hayaatu", watau "Rayuwa" (Life). Malaman Musulunci masana harshen Larabci da ilimin shari'a sun nuna cewa, "Ruhin" dan adam (Human Soul), idan tana cikin jikinsa, ita ce ke wakiltar "zatinsa" ("An-Nafs"), wannan ke sa ya samu "Rayuwa" (Life), har ya zama mai hankali, mai tunani – iya gwargwadon shekarunsa. Da "Fahimta", da "Irada", da "Ilimi", duk suna rataye ne a jikin hankalin dan adam. Daga cikin wadanda suka yi wannan namijin kokari akwai Taajul Lugha, Muhammad ibn Qaasim, wanda aka fi sani da "Al-Ambaari", cikin littafinsa mai suna: "Al-Addhaadu Fil-Lugha," da kuma babban Malamin Lugha, watau "Al-Jarjaanee", cikin littafinsa mai suna: "At-Ta'areefaat."
To, shi kuma "Hankali," wanda ke rataye da ruhin dan adam mai dauke da wadancan al'amura masu ban al'ajabi, a ina yake damfare a jikin dan adam? Daga cikin wadanda suka amsa wannan tambaya akwai Dakta Kareema Mutawalli At-Tookhee, cikin littafinta mai suna: "Quloobun Ya'aqiloona Biha," shafi na 7. Bayan ta kawo ayar da ke Suratul Hajji (aya ta 46), ta bibiye ta da sharhin malaman tafsir, a karshe tace: "Wasu masana suna cewa 'Mahallin hankali shi ne kwakwalwa da ke kai', hujjarsu ita ce, a duk sadda aka daki mutum a ka duka mai karfi, yakan rasa hankalinsa. Amma ingantaccen zance shi ne, zuciya ce ke dauke da hankali, kamar yadda bayanai suka gabata." Wannan shi ne ra'ayin Shawkaani, da Qurtubi, da As-Sa'aalabee da kuma Sheikhul Islam Ibn Taimiyyah; manyan malaman tafisirin Kur'ani. Shi ne kuma ra'ayin Abdullahi dan Abbass (Allah kara masa yarda).
Mako mai zuwa in Allah ya kaimu, za mu kawo bayanai kan sabon nau'in binciken kimiyya da ake kan yi dangane da alakar da ke tsakanin zuciya da kwakwalwa, bayan nan ne za mu sani, a ilimance, wani bangare ne daga cikinsu ke samar da tunani.
Sabuwar Mahangar Malaman Kimiyya kan Zuciya
A makon jiya mun yi bayani kan yadda mahangar Malaman Musulunci suka sha bamban dangane da abin da ya shafi al'amuran zuciya da alakarta da "Hankali" da "Fahimta" da "Ruhi" da kuma "An-Nafs," wato "Zati" ko "Hakikanin" mutum kenan, wajen kokarin fahimtar yadda zuciya ke samar da tunani. A karshe dai bayanai sun nuna mana cewa, yawan ambaton "zuciya" a cikin Kur'ani da Hadisai ingantattu, da yadda Malamai suka ta danganta tasirinta wajen tunani, na nuna lallai akwai wani sha'ani tattare da ita. Duk da cewa malaman kimiyya a baya sun tabbatar kwakwalwar dan adam ce ke samar da tunani, amma ta la'akari da yadda nassoshin Kur'ani suka ta maimaita kalmar "zuciya" ta sa muka ce a yau za mu koma dakin binciken malaman kimiyyar wannan zamani, musamman daga shekaru 20 da suka wuce zuwa yanzu, mu ga ko sun gudanar da wani bincike kan matsayin zuciya dangane da tunani. Domin, kamar yadda na sanar a kashi na 2, nassin Kur'ani ko Hadisi ba su canzawa dangane da abin da suke nuni zuwa gare shi, sai dai rashin dacewar mai bincike kan abin da suke tabbatarwa. Idan suka ce abu kaza, kaza ne, to haka yake. Idan mai bincike ya gano sai mu karbi bincikensa, idan ya gano sabanin abin da suka tabbatar, sai mu ajiye masa sakamakon bincikensa, mu ce masa: "Malam a dai koma dakin bincike, a hankali za a dace." Domin wahayi ba ya canzawa, amma sakamakon duk wani mai bincike yana iya canzawa; dan adam ne shi; tara yake, bai cika goma ba.
Abubuwan da Suka Gano
Malaman kimiyya sun gudanar da bincikensu na farko kan zuciya ne suna masu lura da matsayinta wajen famfon jini zuwa sassan jiki. Wannan mahangar bincikensu na farko kenan, wanda ya ta'allaka ne kacokan kan ayyukan zuciya na "zahiri" wadanda ake iya gani. A marhala ta biyu, sadda aka fara samun yawaitan masu kamuwa da cututtukan zuciya masu alaka da tunani, sai suka sake komawa dakin bincike, inda suka sauya mahanga daga mahangar aikin famfon jini zuwa na fahimtar dalilin da ke haddasa kumburewarta, da kuma haddasa hauhauwan bugawan jini, wanda ke haddasa mutuwa nan take. A nan ne suka gano mummunar tasirin yawan tunani, da bacin rai, da bakin ciki, wajen tauwaye wa zuciya karfin bugawarta da yin aiki yadda ya kamata. To amma kuma, duk da wannan hobbasa da suka yi wajen gano haka, da kokarin samar da magunguna masu magance hauhawan jini wanda ke mummunan tasiri kan zuciya, yawan masu kamuwa da cututtuka masu alaka da zuciya bai ragu ba; sai ma karuwa yake yi a duk shekara, musamman a kasashen da suka ci gaba a fannin tattalin arzikin kasa da siyasa. Sabanin yadda a baya tsofaffi ne galibi ke kamuwa da cututtuka masu alaka da zuciya, yanzu abin ya zama ruwan dare; daga samari zuwa 'yan mata, daga tsofaffi zuwa matasa, daga kasashe masu arziki zuwa kasahe masu fama da talauci. Kai, hatta likitoci sukan kamu da cututtuka masu alaka da zuciya. Tirkashi!
Wannan lamari ne ya sake tilasta wa malaman kimiyya musamman masu lura da yadda zuciya ke gudanar da ayyukanta, da tasirin gazawarta wajen rage tagomashin rayuwa da tattalin arzikin kasa, suka sake komawa dakin bincike don gano hakikanin matsayin zuciya da alakarta da sauran bangororin jikin dan adam, musamman ma kwakwalwarsa. Sanadiyyar wannan sabon tsarin bincike da aka faro tun shekarar 1983 ne aka fahimci abubuwa da dama kan alakar da ke tsakanin zuciya da sauran bangarorin jiki, musamman ma kwakwalwa. Wannan sakamakon bincike da ake kan yi ne na kalato mana a yau, don mu samu wata sabuwar mahanga kan lamarin, kafin yanke hukunci na karshe.
Gamammiyar Alakar Sadarwar Jiki
Abu na farko da aka tabbatar shi ne, akwai gamammiyar alakar sadarwa tsakanin dukkan bangarorin jikin dan adam. Ma'ana, dukkan gabobin jiki suna tarayya da juna wajen musayar bayanai a yayin gudanar da ayyukansu. Daga kwayoyin halittar jiki da ke kaikomo a tsakaninsu (Cells), zuwa sinadaran Hormones da ke samuwa a cikin jiki masu kai-komo a tsakanin bangarorin jiki, duk bincike ya nuna suna dauke ne da bayanai daga wannan bangare zuwa wannan bangare. Wadanda suka fara gano wannan daga cikin masana su ne Dakta Gary E. Schwartz da Dakta Linda Russek ta hanyar wata ka'idar kimiyya mai suna "Dynamic Systems Memory Theory." Daga cikin sakamakon binciken da wannan ka'ida ya hankado shi ne, da "Hankali", da "Fahimta", da "Irada", dukkansu sinadaran makamashin jiki ne masu samuwa ta hanyar musayar bayanai da bangarorin jiki ke yi. Bayan Dakta Gary da Linda da suka tabbatar da wannan ta hanyar bincikensu, har wa yau akwai karin tabbaci da aka samu cikin binciken da Dakta Rollin McCraty da tawagarsa suka tabbatar su ma.
Tasirin Zuciya a Jiki
Abu na biyu da aka sake tabbatarwa shi ne, Zuciya ce ke lura da kuma gyatta dukkan yanayin jikin dan adam; daga kwakwalwa har zuwa yatsun kafafunsa. Domin ita ce kamar babbar na'urar samar da makamshin lantarki zuwa sauran sasannin jiki. A binciken su Dakta Gary Schwartz, sun nuna cewa: "Zuciya ce mabubbugar farko wajen samar da sinadarai da makamashin bayanai a jikin dan adam." An kuma tabbatar da cewa, a duk bugawar zuciya wajen fanfon jini, wannan bugu kan samar da sinadaran lantarki sama da Watt 2, wanda zai iya haska karamin kwai na wutar lantarki. Kuma zuciya ce ke aikin rarraba bayanai daga wannan bangare zuwa wancan, sannan ta karbo daga wani bangare zuwa wani. Duk bangaren da bai samu karban bayanai yadda ya kamata tsakaninsa da zuciya ba, to, ba zai iya gudanar da aikinsa yadda ya kamata ba, kuma wannan zai yi tasiri matuka wajen rage masa tagomashin rayuwa, musamman ta bangaren farin ciki da lumana. Wannan na kunshe ne cikin ka'idar da suke kira: "Psychophysiological Coherence", wacce ke tabbatar da cewa, dan adam na samun kansa a halin "Cikakkiyar natsuwa" ne idan dukkan bangarorin jikinsa suna fahimtar sakon da zuciya ke aika musu ba tare da wata matsala ba. Bayan Dakta Gary, har wa yau an samu tabbaci daga binciken da Cibiyar Gudanar da Bincike kan Aikin Zuciya mai suna HeartMath Institute da ke kasar Amurka ta gudanar, karkashin Dakta Rollin McCraty.
Sadarwa Tsakanin Zuciya da Bangarorin Jiki
Abu na uku da aka sake tabbatarwa karara shi ne, akwai hanyoyi guda hudu da zuciya ke amfani da su wajen aiwatar da sadarwa zuwa sauran sasannin jiki. A cikin sakamakon bincikensu mai shafuka 103, Dakta Rollin McCraty da abokan bincikensa sun zayyana wadannan hanyoyi guda hudu a karkashin babi mai take: "System Dynamics: Centrality of the Heart in the Psychophysiological Network." Hanyar farko ita ce ta hanyar jijiyoyin sadarwa da take dauke dasu, watau "Neurons", wadanda ke aikin musayar bayanai tsakanin zuciya da sauran bangarorin jiki, musamman ma kwakwalwa. Sai hanya ta biyu wacce ta kunshi aiwatar da sadarwa ta hanyar sinadarai masu suna "Hormones." Su sinadaran "Hormones" wasu nau'ukan sinadarai ne da bangarorin jiki ke samar da su, kuma suna dauke ne da bayanan sadarwa daga wanda ya samar da su zuwa bangaren da ake son su isar da sakon gare shi. Zuciya kan samar da wadannan nau'ukan sinadarai masu dimbin yawa, kuma ta hanyarsu ne take aikawa da sakonni ga sauran bangarorin jiki. Hanya ta uku ita ce ta amfani da sautin bugun zuciya da ke samuwa a duk lokacin da jini ya shigo ko yake fita daga zuciyar. Shi kanshi wannan sautin bugun zuciya, wanda suka kira: "Pressure and Sound Waves" an lura cewa akwai bayanai na sadarwa da ke dauke a cikinsa, wanda bangarorin jiki ne kadai ke iya fahimta tare da sarrafa su. Sai hanya ta karshe, wato ta hanyar sinadaran maganadisu, ko "Electromagnetic Field" a harshen malaman kimiyya. Wannan hanya ta karshe na daga cikin abubuwa masu ban al'ajabi da zuciya ke samar da su. Yanayi ne mai dauke da bayanai cikin sinadaran maganadisu, wanda ke bulbulowa daga zuciya, ya game sauran sasannin jiki daga ciki, sannan ya game muhallin da mai zuciyar yake.
A wani gwajin bincike da Dakta Gary da abokiyar aikinsa Linda suka gudanar, inda aka gwama kwayoyin halittar zuciya (Heart Cells) guda biyu na mutane daban-daban a mahalli daya, sakamakon bincike ya tabbatar da samuwar wani "gamammen tsarin musayar bayanai" da ya shiga tsakaninsu da hanyar sinadaran magadisu. Wannan mahallin sinadarin maganadisu da zuciya ke fitarwa asalinsa daga kwayoyin halittu ne da ke cikin zuciyar, watau "Heart Cells". Su wadannan kwayoyin halitta na zuciya, bincike ya nuna cewa a duk sadda zuciya ta buga, wannan bugu kan haifar da makamashin maganadisu da karfinsa zai iya haska dan karamin kwan lantarki. Bayan haka, akwai na'urar gwajin zuciya mai suna "Electrocardiogram" (ECG), wadda ke dauke da wayoyi masu sinsino sinadaran lantarki ko maganadisu daga zuciya, don gano yanayin da zuciya ke ciki, da tsarin bugawarta, da kuma yanayin lafiyarta. Galibi akan dora wadannan wayoyi ne a kan kirji da hakarkarin mara lafiya don fahimtar hakan. Daga baya aka gano ta hanyar bincike da gwaji, cewa a duk inda aka dora su a jikin mutum, na'urar na iya sinsino sinadaran lantarki da maganadisu daga zuciyarsa, saboda gamewarsu; abin da ke nuna karfin tasirin wannan yanayi na zuciya.
Kari a kan haka, bincike na baya-bayan nan kuma ya sake tabbatar da cewa, idan mutum na kwance ko yana zaune, na'urar ECG na iya daukan hoton zuciyarsa da tazarar kafa uku daga inda yake, ba tare da an manna masa wayoyinta a jikinsa ba don darsano sinadaran lantarki da na maganadisu. Wannan ke nuna cewa lallai karfin tasirin zuciya a jikin dan adam ya shallake na kwakwalwa nesa ba kusa ba. Domin na'urar "Electroencephalogram" (EEG) da ake amfani da ita wajen gwajin yanayin kwakwalwa, dole sai an manna wayoyinta a kai da goshin mara lafiya sannan ake hango yanayin bugawa da aikinta. Amma na zuciya kuwa, ko da tazarar kafa uku ne daga inda mara lafiya yake ana iya daukan hoto da ganin yanayin da zuciyarsa ke aiki. Wannan na yiwuwa ne sanadiyyar wannan sinadaran maganadisu da zuciya ke fitarwa, daga cikinta har zuwa waje, wanda malaman kimiyya suka ce yana game mahallin da tazararsa ya kai nisan kafa biyar.
A wani binciken da Cibiyar HeartMath da ke jihar Kalfoniya na kasar Amurka ta gudanar, ya tabbata cewa ta hanyar wannan sinadaran maganadisu mai gamewa, zuciyar dan adam ta kan fahimci hali da yanayin mahallin da take ciki nan take, domin bincike ya nuna cewa ta wannan hanya zukata kan aiwatar da sadarwa a tsakaninsu, ba tare da an yi magana ko jin wani sauti ko kallon wani abu ba. Shi yasa da zarar ka shiga unguwa ko gari ko wani wurin da babu zaman lafiya, nan take za ka sha jinin jikinka, saboda sadarwa da zukata ke yi a tsakaninsu. Wanda ya fara aiwatar da bincike a kan haka shi ne Karl Pribam, ta hanyar wata ka'idar kimiyya da ya kira: "Spetral Domain." A karshe, sakamakon binciken Cibiyar HeartMath ya tabbatar da cewa: yawan damuwa, da bacin rai, da tashin hankali, da bakin ciki, suna rage karfin sadarwar zuciya, da rage tagomashin garkuwar jiki, sannan su rage karfin bugun zuciya wajen aika jini da kashi 5 zuwa 7. A yayin da farin ciki, da kauna, da yafiya, da godiya suke kara karfin maganadisun lantarkin sadarwar zuciya, da sinadaran "Hormones" masu aikawa da sakonnin bayanai daga zuciya zuwa sauran bangarorin jiki, da kara wa garkuwan jiki (musamman sinadaran "White blood cells") karfi, don ba jiki kariya daga warakar cututtukar sankara da sauransu.
A mako mai zuwa in Allah ya yarda, za mu kawo bayanai masu nuna alakar da ke tsakanin zuciya da kwakwalwa ta bangaren sadarwa, daga nan za mu yi hukuncin karshe kan asalin tunani. A ci gaba da kasancewa tare da mu.
I have no special talent. I am only passionately curious.
----Albert Einstein